IQNA

Taron Matasa Musulmi karo Na Biyu A Kasar Kenya

23:51 - November 26, 2017
Lambar Labari: 3482141
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da taron matasa musulmi kar na biyu a birnin Nairobin kasar Kenya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar yada al’adun muslunci cewa, a jiya an gudanar da taron matasa musulmi karo na biyu a birnin Nairobi na kasar Kenya da nufin kara karfafa musulmi kan rikoda koyarwar wannan addini.

Wannan taro mai tak kada ku yane kauna ana gudanar da shi ne a lokacin gudanar da tarukan malidin manzon Allah a cikin wannan wata, kamar yadda aka fara daga skarar da ta gabata.

Dubban matasa musulmi ne suka halarci wurin taron, inda aka gabatar da jawabai kan muhimamncin zaman lafiya da kuma yin hakuri da juna, tsakanin musulmi da ma wadanda ba musulmi ba, tare da yin koyi da manzon Allah a cikin haka.

366719


captcha