IQNA

An Fara Taron Tattalin Arziki Na Halal A Nairobi

20:35 - April 10, 2017
Lambar Labari: 3481393
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani zama kan harkokin tattalin arziki da suka shafi shirin nan na Halal a birnin Nairobi na kasar Kenya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na Standard Media cewa, a yau an fara gudanar da wani zama kan harkokin tattalin arziki na Halal a birnin Nairobi na kasar Kenya da ke gabashin nahiyar Afirka.

Wannan zama zai mayar da hanali kan yadda za akara bunkasa harkokin saka hannayen jari a kamfanonin na halal, wanda kasar Kenya kasa mafi karfin tattalin arziki a gashin nahiyar Afirka za ta fi dacewa da daukar nauyin wannan shiri.

Tun kafin wannan lokacin dai shugaban kasar ta Kenya ya gayyaci manyan jami'ai na bankin muslunci, tare da bada dama ga wannan banki da ya bude rassansa a cikin kasar Kenya, lamarin da ya samu karbuwa daga bankin.

Tsarin tattalin arziki na Halal na da zimmar samar da kuadde da za su kai dala trillion 2 a nan gaba, domin zama daya daga cikin manyan shirye-shirye na tattalin arziki na duniya baki daya.

Yanzu haka wasu daga cikin manyan kasashen duniya sun nuna gamsuwarsu da yadda wannan tsari yake gudana a duniya, inda a mafi yawan kasashen turai da na Asia ake samun kayayyakin halal.

Kasashen Kenya da Tanzania da kuma tsibirin Zanzibar, suna da yawan musulmi da ya ja hankalin masu saka hannayen jari a tsarin kamfanonin halal zuwa ga bude rassansu a cikin wadannan kasashe.

3588515
captcha