IQNA

Limamin Juma'a A Nairobi:

Wajibi Ne Kan Musulmin Kenya Su Shiga Cikin zaben Kasar Da Karfinsu

22:43 - January 29, 2017
Lambar Labari: 3481183
Bangaren kasa da kasa, sheikh Muhammad Sawahilu babban limamamin masallacin Juma'a na birnin Nairobi na kasar Kenya ya kirayi dukkanin musulmin kasar da su shiga cikin zaben kwansu da kwarkwatarsu.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na IQNA ya habarta cewa, sheikh Muhammad Sawahilu babban limamin Nairobi ya jaddada cewa, shiga cikin zabe yana da matukar muhimamnci ga musumin kasar Kenya a dukkanin bangarorinsu na rayuwa.

Ya ce musulmi su zabi 'yan takara da za su kare hakkokinsu a matsayinsu na 'yan kasa kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya kunsa, domin kuwa cewarsa kuri'ar mutane fiye da kashi 30 cikin tana da babban tasiri ga makomar kowane irin zabe ne kuma akowace kasa.

Dangane da batun zaben shugaban kasa kuma, malamin ya ce musulmi su zabi mutumin da suke ganin zai yi wa al'ummar kasar Kenya aiki ba tare da nuna wani banbamci a tsakaninsu ba, kamar yadda kuma ya bayyana cewa babbana bin da yak eda muhiamnc shi ne tabbatar da sulhu da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin dukkanin al'ummar kasar Kenya.

A cikin watan Agustan wanna shekara ta 2017 ce dai za a gudanar da zaben shugaban kasar Kenya gami da na 'yan majalisa.

3567874


captcha