IQNA

Amfani Da Kaloli Wajen Hada kanMabiya Addinai A Kenya

23:45 - August 16, 2016
Lambar Labari: 3480715
Bangaren kasa da kasa, an bullo da wani shiri na hada kan mabiya addinin kiristanci da muslunci ta hanyar yin amfani da kaloli a Nairobi na kasar Kenya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na christiantoday cewa, wurare 20 wannan shiri zai shafa dukakninsu na ibada da suka hada da masallatai da kuma majami’oin mabiya addinin kirista.

Yazmuni Arbulda wani masani kan harkokin zamantakewa dan asalin kasar Amurka, ya bayyana cewa tun a cikin shekara ta 2015 ya dauki alkawalin cewa zai yi amfani da wata hanya ta musamman domin samar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai.

Ya ci gaba da cewa ko shakka babu samar da hanyoyin na zaman lafiya da fahimtar a tsakanin mabiya addinai na daya dag cikin muhimman ayyuka da ya kamata masana su mayar da hankali a kansu a wannan zamani da muke ciki.

Dangane da tasirin kaloli wjen isar da sako, y ace an yi amfani da kaloli wajen gabatar da mahanga kuma hakan ya yi tasirin gaske a bangarori na duniya.

A kan haka ce kasar Kenya tana da matkar muhimamnci ga dukaknin bangarori na mabiya addinai na kiristanci da muslunci, kuma kokarin haifar da rashin fahimta atsakaninsu ba zai yi tasiri ba kamar yadda wasu ke zato, domin kuwa dukkanin bangarorin biyu suna da fahimtar juna na tsawon tarihi.

Kasar Kenya ta askance daya daga cikin kasashen gabashin nahiyar Afirka, akasarin mutanen kasar dai mabiya addinin kirista ne, yayin da musulmi adadinsu bai wuce kasha 15 cikin dari ba.

3523357

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kenya kaloli nairobi musulmi kiristoci sako
captcha