IQNA

Mutanen Najeriya Sun Yi Zanga-Zanga Domin Nuna Rashin Amincewa Da Kisan ‘Yan Shi’a

23:17 - December 18, 2015
Lambar Labari: 3465574
Bangaren kasa da kasa, dubban mutane a biranan kasar Najeriya sun gudanar da jerin gwano domin nuna rashin amincewa da kisan gillar da sojojin kasar suka yi kan mabiya tafarkin shi’a karskashin jagorancin sheikh Ibrahim Zakzaky.


Kamnin dillancin labaran Iqn aya habrat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ala’alam cewa, rahotannin daga Nijeriya sun bayyana cewar dubun dubatan 'yan kungiyar harkar Musulunci a kasar sun fito kan tituna da dama daga cikin biranen kasa a yau Jumu'a don kiran mahukuntan Nijeriya da su sako jagoran kungiyar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da suka kama a ranar Litinin din da ta gabata.



Shafin harkar Musuluncin na internet ya bayyana cewar an gudanar da irin wadannan jerin gwano da gangami ne a garuruwa daban-daban na kasar inda masu jerin gwanon wadanda suke dauke da hotunan Sheikh Ibrahim El-Zakzaky suka bukaci da a sako musu shugabansu da ke tsare a hannun jami'an tsaron kasar.



Shafin ya kara da cewa an dai gama jerin gwanon lafiya ba tare da faruwar wani rikici ba.

Har ya zuwa yanzu dai jami'an tsaron Nijeriyan suna ci gaba da tsare shugaban kungiyar 'yan'uwa musulmin Sheikh Ibrahim El-Zakzaky a wani wajen da ba a tantance ko ina ba ne, duk da cewa babban hafsan hafsoshin sojojin kasa na Nijeriyan Laftanar Janar Tukur Yusuf Burutai ya bayyana cewar tuni sun mika Sheik El-Zakzakin ga hukumar da ta dace don gurfanar da shi a gaban kotun.



Wanda ya jagoranci sallar Juma'ar babban birnin Jamhuriyar Musulunci  yayi kakkausar suka ga kisan gillan da sojojin Nijeriya suka yi wa 'yan kungiyar 'yan'uwa Musulunci ta Nijeriya a birnin Zariya yana mai kiran gwamnatin Nijeriya da ta gudanar da bincike da kuma hukunta wadanda suke da hannu ciki cikin gaggawa.



Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da hudubar sallar Juma'a a yau din nan inda yayin da yake nuna bakin cikinsa da irin dirar mikiyan da sojojin suka yi wa 'yan kungiyar 'yan'uwa musulmi da kuma kashe wani adadi mai yawa, ya ja kunnen gwamnatin Nijeriyan da guji aikata irin wannan danyen aikin wanda yayi daidai da muradin sahyoniyawa, wahabiyawa da kuma kungiyoyin 'yan ta'adda.



Har ila yau Na'ibin limamin Juma'ar ya kirayi gwamnatin Nijeriyan da ta gaggauta sakin shugaban kungiyar Harkar Musulunci a Nijeriya, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da kuma sauran 'yan kungiyar da ake rike da su.



Bayan sallar juma'ar dai an gudanar da jerin gwanon yin Allah wadai da abin da ya faru a Zariyan, kamar yadda kuma aka gudanar da irin wadannan jerin gwanon a garuruwa daban-daban na kasar.



3465552

Abubuwan Da Ya Shafa: nigeria
captcha