IQNA

An Girmama Wani Dan Nigeria A Lokacin Aikin Hajji saboda Gaskiyarsa

23:03 - October 03, 2015
Lambar Labari: 3377998
Bangaren kasa da kasa, an girmama wani wani alhaji dan Nigeria matashi wanda ya tsinci wani tarin kudi a cikin masallacin harami kuma ya mayar da sub a tare da ya taba saboda gaskiyarsa.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar daily Post ta Nigeria cewa, Sulaiman Bello wani matashi dan Nigeria da ya tafi a hajji bana, kuma ya tsinci wani tarin kudi masu yawa a cikin masallacin harami ya nemi mai su ya mayar da su ba tare da ya ci kudinba.

Abdulalhi Muhammad shuhaban hukumar alhazan Nigeria ya nuna godiyarsa matuka dangane da yadda wanann matashi na dan kasarsa ya nuna kyayyawa dabia ta musulunci tare da wakiltar kasar da irin wannan hali.

Sayyid Taher Hashemi daya daga cikin shgabannin hukumar alhazai ta kasar Afghanistan ya bayyana cewa, hakika sun ji dadi dangane da yadda aka samu mutum mai imani haka, wanda ya tsinci kudi masu tarin yawa kuma ya yi kokari ya gano mai su ya bashi abinsa.

Wanna  lamari ya sanya an bayar da tikiti na musamman ga Sulaiman Bello domin ya sake halartar aikin hajjin sheakara mai zuwa, sakamakon dabir da ya nuna a wurin aikin ibada.

3377743

Abubuwan Da Ya Shafa: nigeria
captcha