IQNA

Saboda Matsalar Boko Haram An Hana Addu’oin Lailatul Qadr A Wasu Masallatan Najeriya

23:48 - July 11, 2015
Lambar Labari: 3326794
Bangaren kasa da kasa, saboda matsalolin kungiyar takfiriyya ta Boko Haram a Najeriya an hana gudanar da adduoin lailatl qadr a wasu masallalatai a rewacin Najeriya.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na On Islam cewa, an hana gudanar da adduoin lailatl qadr a wasu masallalatai a rewacin Najeriya sakamakon matsalolin tsaro da ake da danganta da kungiyar yan ta’adda ta Boko Haram da ta addabi al’ummar kasar musamamn bayan harin birnin Kano.

Bayanin ya ci gaba da cewa a cikin makon nan wata yarinya ta nufi wani masallacin birnin da nufin tarwatsa shi da wadanda suke ciki da suke gudanar da salla, kafin isa sai ta tarwatse baki daya, inda ubangiji ya kare bayinsa da suke salla.

Muhammad Abdullah wani limami ne a cikin masallatan birnin ya bayyana cewa hakika abin da yake faruwa a bin bain ciki ne da takaici, kuma saboda wadannan matsaloli aka dauke tarukan na raya dararen qadr kamar yadda ake yi.

Y ace suna rokon Allah madaukakin sarki da ya shiryar da wadanna mutane da shedan ya batar da su idan masu shiryuwa ne, idan kuma ba masu shiryuwa ba ne to Alah ya kawar da su baki daya.

A cikin wannan wata na Ramadan masallatai 3 ne aka kai wa harin bam, mafi muni daga cikinsu shi ne na birnin Jos wanda mutanen kimanin 44 suka rasa rayukansu, wasu da dama kuma suka samu raunuka.

3326716

Abubuwan Da Ya Shafa: nigeria
captcha