IQNA

Dubban Daliban Jami'a A Nigeria Za Su Shiga Wani Shiri Na Kur'ani

16:41 - December 20, 2014
Lambar Labari: 2623525
Bangaren kasa da kasa, dubban daliban jami'a za su shiga cikin wani shiri na samun horo dangane da koyarwa irin ta kur'ani mai tsarki a ranakun hutu da za a samu a karshen wannan wata.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na All Africa cewa, a cikin wannan mako ne aka sanar da cewa dubban daliban jami'a za su shiga cikin wani shiri na samun horo dangane da koyarwa irin ta kur'ani mai tsarki a ranakun hutu da za a samu a karshen wannan wata shekarar girgori da ake bayarwa kamar yadda aka saba.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shiri shi ne irinsa na farko da za a gabatar domin amfanin daliban da suke da sha'awar sanin wani abu dangane da koyarwar kur'ani mai tsarki, duk kuwa da cewa akasarin wadanda za su amfana da shirin dai dama mabiya addinin muslunci ne da suke da sha'awar sanin koyarwar addininsu, wanda kuma wasu daga cikin malaman kasar suka dauki nauyin faraway daga wannan shekara.

Tarayyar najeriya na daya daga cikin kasashen da suka fi yawan musulmi a duniya idan aka kwatanta da sauran kasashe, inda za ta zo ta hudu zuwa ta biya a sahun jerin kasashen da suke da yawan musulmi a duniya, wanda hakan ya sanya take da bababn tasiri a cikin nahiyar Afirka ta fuskar addini, baya ga tasiri ta fuskar tattalin arziki da take da shai, bisa ga kididdiga musulmi da kiristoci a Nigeriya suna 55 da 49 na daga mutane miliyan 140 a kasar.

2623458

Abubuwan Da Ya Shafa: nigeria
captcha