Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na TART na kasar Turkiyya cewa, dakin karatu da wuraren adana kayan tarihi na kasar Masar sun gudanar da wani biki a daidai lokacin da aka kammala dawo da kwafin kur’ani mai tsarki na Hijazi, wanda aka fara a farkon rabin karni na daya na hijira.
Wannan juzu'in kur'ani mai tsarki yana da shafuka 32 kuma ya kunshi shafuka 16 marasa galihu da shafuka 8 da aka rubuta da tawada na karfe.