IQNA

Saka sunayen wasu shugabannin kungiyar 'yan uwa musulmi a cikin jerin sunayen ta'addancin Masar

20:01 - August 04, 2023
Lambar Labari: 3489589
Alkahira (IQNA) Jaridar Al-Waqa'e ta kasar Masar ta buga matakin sanya sunayen wasu shugabannin kungiyar 'yan uwa musulmi a cikin jerin sunayen 'yan ta'adda.

A rahoton shafin yada labarai na "Middle East News", bisa ga wannan yanke shawara, an shigar da wadannan masu laifi cikin jerin sunayen ta'addanci: "Mohammed Badie Abdul Majeed Mohammad Sami, Mohammad Khairat Saad Abdul Latif Al-Shatar, Mohammad Saad Tawfiq Mustafa Al -Katatani, Sayyed Mahmoud Ezzat Ibrahim Ibrahim, Mohammad Mohammad Ibrahim Al-Baltaji, Saad Esmat Mohammad Al-Husseini, Hazem Mohammad Farooq Abdul Khaleq Mansour, Essam Ahmed Mahmoud Al-Hadad, Mohi Hamed Mohammad Al-Sayed Ahmed, Ayman Ali Seyed Ahmed Al -Mutawali, Khalid Saad Hassanein Mohammad, Ahmed Mohammad Mohammad Al-Hakim, Khalil Osama Mohammad Mohammad Al-Aqid, Ahmed Mohammad Mohammad Abd al-Ati, Mohammad Fathi Rifaa al-Tahtawi da Mohammad Ahmed Sheikha.

A watan Disambar shekarar da ta gabata ne kotun hukunta manyan laifuka ta birnin Alkahira na kasar Masar ta sanya kungiyar 'yan uwa musulmi da wasu kungiyoyi 14 cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda na tsawon shekaru 5 bayan bukatar masu gabatar da kara a kasar.

 

4160136

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: musulmi masar kungiya alkahira sunaye
captcha