IQNA

Gambia za ta karbi bakuncin taron ba da tallafin kudi na kasashen musulmi na Afirka

15:05 - February 26, 2022
Lambar Labari: 3486987
Tehran (IQNA) Za a gudanar da taron bayar da tallafin kudade na kasashen musulmi karo na takwas a kasar Gambia, domin duba karfin tattalin arzikin nahiyar.

A cewar Pakistan Observer, an shirya gudanar da taron a dakin taro na kasa da kasa na Sir Dawda Kairaba Jawara a ranar 23 ga Maris, kuma a ci gaba da gudanar da taron bita na kwanaki biyu.
Makasudin wannan taron shi ne yin nazari kan ci gaban kasuwar hada-hadar kudi ta Afirka don fa'idar zamantakewa da tattalin arzikin yankin.
A cewar masu shirya taron, taron zai samar da wani dandali ga masana na Afirka, domin tattauna sabbin dabarun shiga harkokin kudi na Musulunci a fadin yankin.
Mohammad Zubair Mughal, daya daga cikin wadanda suka shirya taron, ya ce yana da kwarin guiwa game da makomar masana'antar hada-hadar kudi ta Musulunci a Afirka.
Ya kara da cewa: "Yanzu lokaci ne mai kyau da za a yanke shawarwarin kudi da suka dace ta hanyar amfani da ra'ayoyin tallafin kudi na Musulunci wajen samar da manufofin tattalin arziki ga gwamnatoci." Shugabannin Afirka suna tafiya a kan hanyar da ta dace don bunkasa yankin.
Za su yi la'akari da muhimmancin tsarin kudi na Musulunci ga manufofinsu na zamantakewa da tattalin arziki.
An gudanar da zaman da ya gabata a Tanzaniya a bara.
 
https://iqna.ir/fa/news/4038743

Abubuwan Da Ya Shafa: gambia afirka musulmi
captcha