IQNA

Baje Kolin Kasuwa Mai Taken Ramadan Bazaar a Canada

21:07 - February 22, 2022
Lambar Labari: 3486973
Tehran (IQNA) Al'ummar Musulmin Winnipeg sun gudanar da bikin "Ramadan Bazaar" na farko bayan shafe shekaru biyu ana fama da barkewar cutar Covid-19.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na CBC cewa, kungiyar musulinci ta birnin Manitoba na kasar Canada ce ta kafa kasuwar.
Raid Hamdam, Shugaba na kungiyar Musulunci ta Manitoba, ya ce da yawa daga cikinsu (masu sayarwa) sun daina aiki saboda barkewar cutar ta Covid kuma wasu an tilasta musu rufe kasuwancinsu. Duk da haka, wasu daga cikinsu sun dawo kasuwanci, don haka muna fata mafi kyau a gare su.
Daga cikin kayayyakin da ake sayar da su a wannan kasuwa har da kayayyakin da ake kerawa na gida da kuma kayayyaki kamar su Alkur’ani, da littafan addu’o’i, da tufafin Musulunci da ke da wuyar shiga.
Kungiyar Musulunci ta Manitoba ta kan bude wannan kasuwa duk shekara kafin Ramadan, kuma mafi yawan wadannan kasuwannin na shirin budewa a bana.
 
 
https://iqna.ir/fa/news/4037764

Abubuwan Da Ya Shafa: canada Ramadan Bazaar
captcha