Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga majiyoyin gwamnatin Falastinu cewa, duk da irin matakan da Isra'ila ta dauka na hana matasa da masu matsakaicin shekaru zuwa sallar Juma'a a masallacin Quds, amma duk da hakan sama mutane dubu 45 ne suka yi sallar Juma'a a yau a masallacin mai alfarma.
Majiyoyin suka ce, jami'an tsaron Isra'ila dauke da muggan makamai sun kafa shingaye a ko'ina domin hana musulmi gudanar da ibadar sallar Juma'a, wanda hakan bai karya zuciyar musulmin Falastinu ko kange daga ibada ba.