IQNA

Majalisar Iran Ta Amince Da Sunayen Ministocin Da Ra'isi Ya Mika Mata

18:36 - August 25, 2021
Lambar Labari: 3486238
Tehran (IQNA) Majalisar dokokin kasar Iran ta amince da sunayen ministocin da shugaba Ibrahim ra’isi ya gabatar mata, in banda sunan sunan ministan ilimi wanda bai samu amincewar majalisar ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a zaman da majalisar dokokin Iran ta gudanar a yau wanda a kuma shi ne na karshea  zaman tantance sunayen ministocin da Ra’isi ya gabatar mata, ta amince da sunayen baki daya, in banda sunan ministan ilimi.

Shugaba Ra’isi ya jinjna wa ‘yan majalisar kan kokarin da ya ce sun yi wajen ganin sun bin diddigin dukkanin sunayen da ya gabatar domin tabbatar da dacewarsu ko akasin hakan.

Ya ce amincewar da majalisa ta yi da wadannan ministoci ya zo ne bisa gamsuwa da irin kwarewarsu da kuma gogewarsu a bangaren ayyukansu, kuma ya ce yana da tabbaci kan irin kwazon da suke da shi, da kuma kwazon da za su nuna wajen yi wa kasarsu da al’ummarsu aiki.

Sannan ya jaddada cewa, gwamnatin da za a kafa gwamnati ce ta al’ummar kasar Iran baki daya, saboda haka ba za ta yi kasa a gwiwa wajen aiwatar da dukkanin abin da ya rataya a kansu.

Haka nan kuma Ra’isi ya kara nanata aniyarsa ta yin aiki wajen magance matsaloli da dama da kasar take ciki, musamman ma a bangaren tattalin arziki, inda ya ce Iran za ta bayar da muhimmanci wajen gudanar da ayyukan kasuwanci da bunkasa tattalin arziki.

 

3993132

 

captcha