IQNA

Bashar Assad Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Syria

22:46 - May 28, 2021
Lambar Labari: 3485957
Tehran (IQNA) Shugaban Bashar Assad, na Siriya, ya lashe zaben shugabancin kasar a karo na hudu.

Wannan nasara da shugaba Assad ya samu, zai ba shi damar ci gaba da shugabancin kasar na tsawon wa’adin mulki na shekaru bakawai masu zuwa.

Shugaban majalisar dokokin kasar Hamoudeh Sabbagh, ya ce Bashar Assad ya lashe zaben ne da kaso 95.1 na kuri’un da aka kada, sabanin kuri’u kaso 88.7 na shekarar 2014.

A ranar 17 ga watan Yulin 2000 ne shugaba Assad ya maye gurbin mahaifinsa Hafez Assad a matsayin shugaban kasa.

Karkashin kundin tsarin mulkin kasar na shekara ta dubu biyu da sha biyu,  shugaban kasa na da damar tsayawa takara sau biyu, wanda ke nufin, wannan ne wa’adin shugaba Assad na karshe.

3974114

 

 

 

captcha