IQNA

An Fara Shirye-Shiryen Ziyarar Paparoma Francis A Kasar Iraki

23:35 - February 12, 2021
Lambar Labari: 3485643
Tehran (IQNA) a kasar Iraki an fara shirye-shiryen ziyarar jagoran mabiya addinin kirista na darikar katolika na duniya wadda ita ce ta farko a tarihi.

Rahotanni daga kasar ta Iraki sun ce wata tawagar fadar Vatican ta isa birnin Najaf domin tsara yadda ganawa za ta kasance tsakanin Paparoma da kuma bababn malamin addini na kasar Iraki Ayatollah Sayyid Ali Sistani.

Ofishin jakadancin Iraki a Vatican da kuma majiyoyin fadar ta Vatican sun bayyana cewa, a yayin ganawa tsakanin manyan jagororin biyu, za a rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyi, da suka hada da wajabcin girmama juna da ‘yan uwantaka tsakanin ‘yan adam, da kuma yin Allawadai da duk wani nau’in ta’addanci a kan ‘yan adam, da kuma karfafa tattaunawa tsakanin addinai na duniya, musamman kiristanci da muslunci.

Ziyarar Paparoma a Iraki za ta fara ne a  ranar 5 ga watan Maris mai kamawa, inda zai samu taba daga firayi ministan Iraki Mustafa Alkazimi a filin sauka da tahsin jiragen sama na Bagdad, daga nan kuma zai nufi fadar shugaban kasar Iraki, inda zai gana da shugaban kasar Barham Saleh, da kuam wasu manyan jagororin mabiya addinin kirista, da kuma ziyartar wasu majami’oi.

A ranar 6 ga wata kuma zai nufi birnin Najaf, inda zai gana da Ayatollah Sayyid Ali Sistani, daga nan kuma zai wuce zuwa lardin Ziqar, inda zai ziyarci yankin da aka haifi annabi Ibrahim (AS) bayanan kuma a ranar 7 ga wata zai isa birnin Arbil, daga nan kuma zuwa Mosil inda zai ziyarci majami’ar kiristoci ta tarihi wato Hus Al-bai’ah.

 

3953514

 

captcha