IQNA

Ansarullah Ta Yemen Da Gwamnatin Hadi Sun Cimma Matsaya Kan Musayar Fursunoni

23:18 - September 27, 2020
Lambar Labari: 3485222
Tehran (IQNA) bangarorin Ansarullah da gwamnatin Hadi mai ritaya a Yemen sun amince kan yin musayar fursunoni .

Wata majiya a tawagar gwamnatin Yemen mai murabus data bukaci a sakaya sunanta, ta shaidawa kamfanin dilancin labaran Faransa cewa an cimma matsaya ta musayar fursunoni dubu daya da tamanin kuma nan da makwanni masu zuwa za’a aiwatar da yarjejeniyar, inda za’a sallami sojoji dari hudu, ciki har da na kawancen da Saudiyya ke jagoranta, sai kuma mayaka daga bangaren Ansarullah dari shida da tamanin da daya.

Wasu bayanai na daban sun ce yau Lahadi ake sa ran kammala tattaunawar, inda kuma za’a sanar da yarjejeniyar da aka cimma, kuma daga cikin fursunonin da ake son sallama har da wani dan uwa ga shugaban kasar mai murabus Abedrabbo Mansur Hadi.

Game kuma da bukatar sakin Janar Nasser Mansour Hadi, ‘yan Houtsi sun jinkirta sakin nasa.

Idan dai har wannan musayar ta tabbata, zata iya kasance wata musayar fursunoni mafi yawa a tsakaninsu tun bayan yakin da barke a kasar a cikin shekara dubu biyu da sha biyar.

Wannan dai na daga cikin yarjejeniyar zaman lafiya da bangarorin biyu suka cimma a shiga tsakanin majalisar dinkin duniya .

 

3925669

 

 

captcha