Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya ne aka bude makarantar koyon hardar kur’ani mai tsarki a yankin Daryush na kasar Moroco, ta Azalaf wadda cibiyar kur’ani ta Badr ta dauki nauyin budewa.
Bayanin ya ce taron bude makarantar ya samu halartar masana da jami’an gwamnati gami da malaman addini da kuma malaman jam’a da sauran masu hannu da shuni, gami da sauran mutanen gari, kamar yadda limamai na masalatai a yankin sun samu halarta.
Babbar manufar kafa wanann makaranta dai itace horar da matasa karatu da hardar kur’ani mai tsarki, wadda kuma tana da alaka ne da mabiya darikar Daryush na kasar morocco.