IQNA

Dokar Trump Ta Shafi Musulmin Kasar Canada

23:29 - August 31, 2019
Lambar Labari: 3484002
Bangaren kasa da kasa, jami’an huldar diflomasiyyar Amurka a Canada sun hana wasu musulmin kasar ta Canada su 6 tafiya Amurka.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labara Anatoli ya bayar da rahoton cewa, ofishin jakadancin kasar Amurka a Canada ya hana asu muuslmi 6 izinin shiga kasar Amurka.

Rahoton ya ce wannan na daga cikin irin matakan da mahukuntan kasar Amurka suke dauka nea  kan musulmi a cikin lokutan nan, duk kuwa da cewa wadannan musulmi babu wanda ya fito daga daya daga cikin kasashen da Amurka ta haramta wa ‘yan kasa shiga kasarta.

Masu rajin kare hakkokin ‘yan adama  akasa ta Canada sun bayyana wannan mataki da cewa na wariya ne, domin kuwa dukkanin wadannan mutane ‘yan kasar Canada ne ad suke dauke da fasfo na kasar, amma aka hana su izinin shiga Aurka saboda su musulmi ne.

Dawud Ali wani lauya ne muuslmi dan kasar ta Canada, ya bayyana cewa a ‘yan makonnin da suka gabata sun samu wasu koke-koke makamanta hakan, inda aka hana wasu musulmin shiga kasar Amurk daga Canada.

3838749

 

 

 

captcha