IQNA

Jami'an Tsaron Sudan Sun Kashe Masu Zanga-Zanga

23:57 - July 04, 2019
Lambar Labari: 3483806
Akalla Mutum bakwai suka rasa rayukansu yayin da jami'an tsaron Sudan suka afkawa masu zanga-zangar nuna adawa da Majalisar Sojin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Iqna  ya habarta cewa a marecen ranar lahadin da ta gabata, al'ummar kasar sudan sun amsar kiran da kungiyoyin 'yan adawa suka kira na gudanar da zanga-zangar da suka kira ta milyoyin jama'a domin ci gaba da bijirewa Majalisar soja dake rike da madafun ikon kasar

Bayan birnin Khartoum, daga cikin lardunan da aka gudanar da zanga-zangar har da Atbara dake arewaci, da kasla ta gabashi da kuma Abyad dake yammacin kasar ta Sudan.

'Yan kasar Sudan din dai na neman Majalisar Sojan kasar su mika milki ga hanun farar hula, to saidai jami'an tsaro sun yi amfani da karfi wajen tarwatsa mahalarta zanga-zanga tare da kashe akalla mutum bakwai da kuma jikkata wasu dari da tamanin da daya na daban.

Duk da irin wannan zanga-zangar da al'ummar Sudan ke yi, Majalisar Sojin kasar ta ki amincewa da amsa bukatar al'ummar kasar to saidai ta ce a shirye take ta koma kan tebirin tattaunawa da bangaren 'yan adawa kamar yadda ta sanar a ranar lahadin da ta gabata.

A bangare guda kuma Majalisar Sojan ta yi da'awar dakile wani juyin mulki da wasu Sojojin kasar suka so yiwa Majalisar Sojin kasar. wannan kuma shi ne kawo na biyu da majalisar Sojin Sudan ke da'awar dakile yunkurin juyin milki tun bayan da hau kan karagar milkin kasar.

3824400

 

captcha