IQNA

Guterres Ya Kirayi Gwamnatin Myanmar Da Ta Saki ‘Yan Jaridar Da Ta Tsare

23:19 - September 04, 2018
Lambar Labari: 3482952
Babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Gutrres ya bukaci gwamnatin Myanmar da ta sake yin nazari kan hukunci da aka yanke a kan 'yan jarida biyu a kasar.

 

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, babban sakataren na majalisar dinkin duniya ya bukaci a sake yin nazari kan hukuncin da aka yanke wa 'yan jaridar, wadanda aka kame su sanadiyyar aikinsu, inda aka yanke musu hukuncin daurin shekaru 7 a gidan yari.

Shi ma a nasa bangaren kwamitin kare hakkokin bil adama na majalisar dinkin duniya ya yi kakkausar suka kan tsare wadannan 'yan jarida biyu na Reuters, tare da yin kira da a gaggauta sakinsu ba tare da wani sharadi ba.

'Yan jaridar biyu wato Wa Lone da kuma Kyaw Soe Oo, an kame su ne tuna  cikin watan Disamban 2017, sakamaon binciken da suke gudanarwa kan kisan kiyashin da aka yi wa musulmin Rohingya a kasar, inda suka harhada bayanai masu yawa kan batun, abin da ya bakanta ran mahukuntan kasar ta Myanmar.

3743853

 

 

 

 

captcha