IQNA

Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama Ta Bukaci A Hukunta Sojojin Myanmar

23:58 - June 27, 2018
Lambar Labari: 3482790
Bangaren kasa da kasa, Kungiyar ta Amnesty ta zargi kwamandojin sojojin kasar ta Myanmar da tafka laifukan yaki akan al'ummar musulmin Rohingya

 

Kamfanin dilalncin labaran iqna, wani babban jami'i a kungiyar ta kare hakkin bil'adama Matthew Wells yana cewa; Laifukan da kwamandojin sojan kasar Mayanmar suka tafka akan musulmi sun kunshi kisan kiyashi, fyade, azabtarwa,da kone gidaje.

Jami'in kungiyar ta "Amnesty" ya kara da cewa; Da akwai shaidu masu yawa akan laifukan da aka aikata, kuma laifi ne tsararre akan al'ummar Rohingya.

Kungiyar tana da bayanai da ta tattara daga mutane fiye da dari hudu akan laifukan da aka aikata akan al'ummar musulmin Rohingya.

 

3725875

 

 

 

 

 

 

captcha