IQNA

Tarayyar Turai Ta Bukaci A Kare Fararen Hula A Yankin Kachin Na Myanmar

22:40 - February 26, 2018
Lambar Labari: 3482432
Bangaren kasa da kasa, kungiyar tarayyar turai ta yi kira da a kae rayukan fararen hula a kasar Myanmar a yankin Kachin da ke arewacin kasar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na Alshuruq cewa, kungiyar tarayyar turai ta yi kira da a kare rayukan fararen hula a kasar Myanmar a yankin Kachin da ke arewacin kasar sakamakon barazanar da suke fuskanta daga masu tsatsauran ra’ayin addini buda.

Bayanin ya ce akwai dubban ‘yan kabilar Rohingya da suka kauracewa yankunansu a yanin Rakhin zuwa Kachin a rewacin Myamar, ida a halin yanzu haka suke fuskantar wani isan kiyashi daga ‘yan addinin buda masu tsatsauran ra’ayi.

Musulmi ‘yan kabilar Rohingya sun fuskanci kian kiyashia  cikin shekarar da ta gabata daga dakarun gwamnatin Myanmar da kuma ‘yan addinin buda, ba tare da kasashen musulmi ko manyan kasashen duniya sun iya taka musu birki ba.

Yanzu haka akwai sama da muuslmin Rohingya dubu dari shida a cikin Bangaladash da suke gudun hijira domin tsira da rayukansu.

3694816

 

 

 

captcha