IQNA

Ranar Hijabi Ta Duniya A Antario

23:50 - January 31, 2018
Lambar Labari: 3482353
Bangaren kasa da kasa, musulmin garin St Catharines na jahar Antario na kasar Canada sun gudanar da bukukuwan ranar hijabi ta duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na St Catharines Standard cewa, muuslmi na jahar Antario a karon farko sun gudanar da tarukan ranar hijabi.

An bayar da hijabai kimanin 200 ga mata musulmi domin raya wannan rana, kamar yadda kuma a masallatai aka gudanar da tarukada suka kebanci mata zalla.

Daga cikin muhimamn abubuwan da ake tunatar da mata a kansu a wannan rana har wayar da kansu kan muhimmancin da ke tattare da saka hijabi da tasirinsa wajen kare muuncin mace.

Wasu daga cikin mata wadanda ba musulmi ba ne da lamarin ya burge su, sun halarci wuraren da mata musulmi suke gudanar da tarukan, inda sukan karbi mayafi suna lullube kansu suna masu nuna goyon bayansu ga musulmi.

Kasar Canada na daga cikin kasashen da msuulmi suke samun damar gudanar da harkokinsu na addini cikin sauki ba tare da tsangwama ba, amma bayan zuwan sabuwar gwamnatin Amurka, a halin yanzu tasirin kyamar msuulmi a Amurka ya fara shafar musulmin Canada, sakamakon siyasar sabuwar gwamnatin ta Amurka.

3686864 

 

 

 

 

captcha