IQNA

Tunawa Da Mai Tarjamar Kur'ani Na Senegal

16:37 - January 30, 2018
Lambar Labari: 3482348
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da taron tunawa da sheikh Mukhtar Kal Dramah wanda ya tarjama kur'ani mai tsarkia kasar Senegal.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a jiya an gudanar da zaman taro na tunawa da sheikh Mukhtar Kal Dramah wanda ya tarjama kur'ani mai tsarkia  kasar Senegal wanda ya rayu tsakanin 1790-1874.

Wannan malami ya shahara a wurin al'ummar kasar ta Senegal kan hidimar da ya yi ma al'ummar kasar wajen wajen yada ilimin kur'ani mai tsarki.

Daga cikin muhimman ayyukan da ya yi har da tarjama kur'ani mai tsarki a cikin harshen wolof da ake ake magana da shi a kasar, wanda miliyoyin jama'a suke amfana da wannan tarjama tasa.

Sheikh Mukhtar Kal shi ne mahaifin sheikh Dokta Jim Daramah, daya daga cikin fitattun malaman addini na kasar Senegal, wanda ya halarci bababn taron hadin kan musulmi na duniya a kasar Iran, kamar yadda kuma ya ziyarci ofishin kamfanin dillancin labaran kur'ani na IQNA.

Sheikh Mukhtar shi ne ya kafa cibiyar Darul Imam Mukhtar Kal ta kur'ani a kasar Senegal wadda ta yaye dalibai masu tarin yawa a cikin kasar ta Senegal da kuma Gambia.

Al'ummar kasar Seneal suna tunawa da wannan babban malami da ya yi wa kur'ani mai tsarki hidima.

3686644

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna senegal tarjama gambia sheikh mukhtar kal
captcha