IQNA

Musulmi Na Farko A Rundunar Sojin Saman Ingila

22:46 - January 25, 2018
Lambar Labari: 3482334
Bangaren kasa da kasa, muuslmi na farko daga yankin Hilsea na gundumar Portsmouth a kasar Ingila ya shiga aikin soji a rundunar sama ta kasar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na portsmouth.co.uk ya bayar da rahoton cewa, Abrima Jallo muuslmi dan shekaru 34 dan asain kasar Gambia ya hade da rundunar sojin sama ta Ingila.

Ya ce tun yana a Afirka yake mafarin shiga aikin soji, saboda haka a halin yanzu da ya samu wannan damar abin farin ciki ne a gare shi, duk da cewa yana da kalu bale mai yawa a gabansa bayan shiga wannan aiki.

Ya ce a halin yanzu babbar matsalar da yake fuskanta ita cea  bangaren abinci, inda yakan yi kokari ya kiyaye abincin da yake halal a addinin muslunci, yayin da sau da yawa wasu abinci sukan kunshi naman alade, wanda hakan yasa wasu lokuta ba zai iya cin abinci ba, sai dai ya ci ganye, domin ba zai iya cin abincin da musulunci ya haramta ba.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, duk da cewa shi ne musulmi na farko da ya shiga rundunar sojin sama ta Birtaniya, amma kuma a lokaci guda yana kokarin ganin ya kiyaye dukkanin lamurran ibadarsa ta muslunci, duk da cewa abokan aikinda baki dayansu ba musulmi ne ba.

Jonathan Old shi ne babban kwamanda da ke kula da rundunar da Jallo yake ciki, ya bayyana cewa hakika Jallo mutum ne mai tsari, kuma yana da gaskiya, kuma shigarsa wanann aiki zai zama abin misali ga sauran marassa rinjaye a Birtaniya.

 

3685303

 

captcha