IQNA

Kyamar Musulmi Ta Karu A Kasar Amurka

23:56 - November 21, 2017
Lambar Labari: 3482123
Bangaren kasa da kasa, wata kididdiga ta yi nuni da cewa kyamar da ake nuna wa musulmi a kasa Amurka ta karu fiye da kashi dari cikin dari.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na World Religion News ya habarta cewa, wani binci da aka gudana kakashin cibiyar pio, ya nuna cewa kyamar da ake nuna wa musulmi a kasa Amurka ta karu fiye da kashi dari cikin dari a cikin shekaru sha biyar.

Sakamakon binciken ya nunacewa a sekara ta 2001 an kai hari kan musulmi sau 93, har zuwa shekara ta 2015 inda aka samu hari kan musulmi sau 91, wanda hakan ya nuna ruguwar lamarin.

Amma abin mamaki shi ne a cikin skara ta 2016, kada an kai hari akn msuulmi a cikin kasar Amurka har sau 217, wanda hakan ya nuna cewa lamarin ya haura har fiye da kashi dari.

Canjin gwamnati da aka samu a kasar ne yay i tasiri matukar wajen haifar da wannan yanayin kamar yadda masana suke bayyanawa.

Sabbin mahukuntan an Amurka sun zo ne da sunan kyamar musulunci da bakin haure masu ci rani a kasar, musamman ma musulmi daga cikinsu.

3665356


captcha