IQNA

Shugaba Raihani A Taron UN:

Iran Za Ta Mayar Da Martani Kan Karya Yarjejeniyar Nukiliya

13:45 - September 21, 2017
Lambar Labari: 3481917
Bangaren siyasa, Shugaban Hassan Ruhani na kasar Iran ya bayyana jawabin da shugaban kasar Amurka Donald Trump yayi a babban zauren majalisar dinkin duniya a jiya Talata da cewa, jawabin na trump ya kaskantar da kasar Amurka ne a gaban kasashen duniya.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya bayar da rahoton cewa, Shugaban ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar a babban zauren MDD a dazu-dazun nan, ya kuma kara da cewa yerjejeniyar shirin nukliyar kasar Iran da ta cimmawa tare da manya manyan kasashen duniya a shekara ta dubu biyu da sha biyar, yerjejeniya ce ta kasa da kasa, wadda har ma kwamitin tsaro na MDD ya maida ita kuduri, don haka karya wannan yarjejeniya daga bangaren Amurka zai cutar da Amurka ne ita kadai, domin dukkanin kasashen duniya suna mutunta yarejejeniyar.

A wani bangare na jawabinsa shugaba Ruhani ya bayyana cewa, mutanen kasar Iran basu bukaci wani abu fiye da adalci da kuma 'yancida samun ci gaba ba. Don haka ba zata fara karya alkawarin da ta dauka da wadannan kasashe ba, amma kuma idan sauran bangarorin suka karya nasu alkawarin Iran zata maida martanin da ya dace.

Dangane da matsalolin kasashen Yemen Bahrain, Myanmar da Afganistan kuma, shugaban ya ce kada kasashen da suke da hannu wajen jefa su cikin yaki da tashe- tashen hankula, su yi zaton cewa su ma zasu zauna cikin zaman lafiya da ci gaba na lokaci mai tsawo lokaci.

A bangare guda kuma Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya kore yiyuwar tattaunawa da Amurka yana mai cewa tattaunawa da ita bata lokaci ne kawai don kuwa ba ta aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma da ita.

Shugaba Ruhanin ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da manema labarai a bayan fagen taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na sabain da biyu da ke ci gaba da gudana a a helkwatar MDD da ke birnin New York, inda ya ce babu wata tattaunawa da za a yi da Amurka a daidai lokacin da Amurkan take magana kan ficewa daga cikin yarjejeniyar nukilyan da ake cimma da ita da wasu manyan kasashen duniya.

Shugaban kasar ta Iran ya ci gaba da cewa: Mun dau shekaru muna tattaunawa da Amurka kan shirin nukiliyanmu, to amma a yau sai ga shi Amurkawa suna batun ficewa daga cikin yarjejeniyar. A saboda haka da wani dalili ne za a ci gaba da tattaunawa da Amurka a kan sauran batutuwa?

Shugaba Ruhanin dai ya ce Iran tana da wasu zabi da kuma matakan da za ta dauka matukar dai Amurka ta ki girmama wannan yarjejeniya.

3644302


captcha