IQNA

Shirin Bayar Da Horo Kan Bankin Muslunci A Gambia

21:03 - August 09, 2017
Lambar Labari: 3481783
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani shiri na bayar da horo kan ayyukan bankin muslunci a kasar Gambia, wanda cibiyar kula da harkokin kudi da ayyukan tattalin arziki ta yammacin Afirka WAIFEM ta dauki nauyin shiryawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, shafin yada labarai na allafrica ya bayar da rahoton cewa, babbar manufar gudanar da wannan shiri ita ce, bayar da horo ga wasu daga cikin ma'aikatan bankuna na kasar Gambia kan yadda bankin mulsunci ke gudanar da ayyukansa, da kuma yadda bankunan kasar za su iya yin mu'amala da wannan banki.

Wwakilin babban bankin kasar ta Gambia a wurin taron ya bayyana cewa, an gudanar da horon ne har tsawon kwanaki biyar wanda aka kammala jiya, kuma babban abin da aka bayar da muhimamnci a kansa shi ne sanin muhimman ka'idoji na muslunci da bankin yake yin amfani da su wajen hada-hadar kudade, da kuma yadda za a kiyaye haka a yayin mu'amala da wannan banki.

Ya kara da cewa, ko shakka babu kasar Gambia za ta amfana matuka da wanann banki, musamman ganin yadda wasu masu manyan hannayen jari a bankin suka nuna sha'awarsu kan saka hannayen jari a kasar ta Gambia ta haynar wannan banki, wanda hakan zai taimaka tattalin arziki kasar da kuma kara samar da guaraben ayyukan yi.

3628573


captcha