IQNA

Firayi Ministan Australia Bai Amince Da Nuna Wa Musulmi Kyama Ba

19:34 - March 24, 2017
Lambar Labari: 3481342
Bangaren kasa da kasa, firayi ministan kasar Australia Malcolm Turnbull tare da wasu ministocinsa sun ki amincewa da yunkurin Pauline Hanson na kyamar musulmi.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar «Sydney Morning Herald» cewa, firayi ministan Australia ya fito karara ya nuna rashin gamsuwarsa da duk wani yunkuri na wasu ‘yan siyasa ko wasu gungun jama’a na kasar kan kyamar musulmi.

Wannan ya biyo bayan abin da wata fitacciyar ‘yar siyasar kasar ta Australia Pauline Hanson ta yi ne, inda ta yi rubutu a takarda kan cewa a yi addu’a kan a kori musulmi daga cikin kasashen turawa domin kawo karshen ayyukan ta’addanci da suke faruwa.

Matar dai ta yi rubutun ne a cikin kalmomi kamar haka; (# pray 4 muslims ban) wato a yi addu’a kan a samu nararar korar muuslmi tare da haramta musu shiga cikin kasashen turai, ta yi wannan ne kuwa jim kadan bayan kai harin birnin Londona daren laraba.

A daya bangaren masu mayar mata da martani suna rubuta (# prayforLondon) wato a yi addu’a Allah ya kawo zaman lafi a London yak are birnin daga hare-haren ‘yan ta’adda, ma’ana wato harin aikin ‘yan ta’adda ne ba aikin musulmi ba.

Turnbull firayiministan kasar Australia ya bayyana cewa, nuna kyama ga wani bangare na jama’a ko addini ko wata akida saboda abin da wasu ‘yan kalilan da cikin masu danganta kansu da wannan gungun jama’a suka aikata, yin hakan yana tattare da babban hadari, saboda haka ya ce baya goyon bayan kyamar musulmi, domin kuwa su ma ta’addancin yana cutar da su.

3585532

captcha