IQNA

Cire Siffar Musulunci Daga Cikin Sunan Kasar Gambia

16:51 - January 30, 2017
Lambar Labari: 3481184
Bangaren kasa da kasa, Shugaban kasar Gambia Adama Barrow ya bayyana cewa zai cire siffar muslunci daga cikin sunana kasar ta Gambia.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na IQNa ya habarta cewa, Shafin yada labarai na Sabil ya habarta cewa, a jawabinsa na farko a jiya bayan da ya shiga cikin kasar Gambia bayan ficewar Yahya Jammeh, Adama Barrow ya bayyana cewa zai canja sunan kasar.

Ya ce Yahya Jammeh tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar ya canja sunan kasar Gambia zuwa jamhuriyar musulunci domin ya wanke kansa daga barnar da yake aikatawa da sunan muslunci, ya ce wannan ya kawo karshe.

Adama Barrow bisa la'akari da cewa mafi yawan al'ummar kasar Gambia musulmi ne ba zai yiwu a cire al'adu da addinin muslunci daga harkokin jama'a na kasar ba, amma ba za a yi amfani da sunann muslunci domin cimma wasu manufofi na siyasa ba.

Tsohon shugaban kasar Gambia Yahya Jammmeh dai ya kwashe tsawon shekaru 32 yana mulkin kasar, inda ya sha kayi a zaben da aka gudanar a kasar a cikin watan Disamban shekarar da ta gabata.

3567970


captcha