IQNA

Mahukuntan Mayanmar Za Su Kori Musulmi Daga Yankunansu

21:17 - December 27, 2016
Lambar Labari: 3481075
Bangaren kasa da kasa, Gwamnatin kasar Myanmar na shirin raba wasu musulmi da yankunansu, tare da zaunar da wasu 'yan addinin Buda a cikin yankunan nasu a garin Mangdo da cikin lardin Rakhin.
Kamfanin dilalncin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Arakan ya bayar da rahoton cewa, mahukunta a lardin Rakhin na kasar Myanmar, sun gina wasu kauyuka guda bakwai a wasu yankuna da ke cikin lardin na Rakhin, da nufin zaunar da musulmi da suke a garin Mangdo.

Mahukuntan suka ce asalin garin Mangdo na mabiya addinin Buda ne, amma daga bisani 'yan kabilar Rohingya da suka shigo cikin kasar daga Bangadasha suka zauna wurin, a kan haka mabiya addinin Buda za su dawo wurinsu, yayin da muuslmin da ke wurin za a mayar da su zuwa kauyukan da aka gina musua wasu wuraren na daban.

Fiye da kashi 98 na mutanen da suke zaune a wannan gari dai mabiya addinin muslunci ne 'yan kabilar Rohingya, yayin da adadin masu bin addinin Buda a garin bai wuce kashi 2 cikin dari ba, kuma muuslmi suna zaune da su lafiya tsawon daruruwan shekaru ba a taba jin tsakaninsu.

Kimanin watanni da suka gabata ne dai jami'an tsaron gwamnatin Myanmar suka yi wa musulmi kisan gilla a wannan yanki, tare da kone musu gidaje da kaddarori.

3557068


captcha