IQNA

Netanyahu Na Shirin Sake Mika Daftarin Kudirin Dokar Hana Kiran Sallah

22:51 - December 10, 2016
Lambar Labari: 3481021
Firayi ministan haramtacciyar kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu na shirin sake mika daftarin kudirin dokar hana yin amfani da lasifika a wuraren ibada da dare musamman kisan salla, domin majalisar Knesset ta amince da hakan.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, Jaridar Haaretz ta haramtacciyar kasar Isra'ila ta bayar da rahoton cewa, Netanyahu tare da wasu yahudawa 'yan siyasa masu tsatsauran ra'ayi, suna shirin sake mika daftarin kudirin dokar hana yin amfani da lasifika a wuraren ibada a cikin Quds da sauran yankunan Palastinawa da Isra'ila take mamaye da su, daga kimanin karfe 10 na dare zuwa 7 na safe, musamman a masallatan musulmi.

Tun kafin wannan lokacin an shirya wannan daftarin kudiri da nufin kada kuri'a a kansa a majalisar Knesset, amma saboda wasu dalilai aka dakatar da kada kuri'ar, wanda ahalin yanzu Netanyahu da mukarrabansa za su gabatar da shi, wanda kuma ake sa ran zai samu amincewar 'yan majalisar masu tsatsauran ra'ayi da ke mara baya ga Netanyahu.

Kasashen larabawa da na msuulmi da dama sun yi Allawada da wannan daftarin kudiri, tare da bayyana shi a matsayin daya daga cikin hanyoyin cin zarafin palastinawa musulmi, wasu daga cikin majami'oin mabiya addinin kirista da ke cikin yankunan Palastinawa da Isra'ila ta mamaye, sun rika saka kiran sallar asuba, domin nuna goyon bayansu ga musulmi.

3552480


captcha