Ya ce ba ma shi kadai ba, hatta ga sauran dalibai musulmi da suke son su yi salla babu wuri, domin kuwa salla baban rukuni na addainin muslunci, kuma duk inda msuulmi yake a lokacin salla yana bukatar wuri domin yin salla, amma babu yadda zai dole sai ya shiga a tsakanin hanyoyin da ke cikin dakin karatu a nan yake yin salla.
Charles Kimbal shi ne babban darakta na bangare nazatri kan addinin muslunci a jami'ar, ya bayyana cewa hakika samar da wurin salla ga msuulmi lamari ne mai matukar muhimmanci, kuma ya ji dadin hakan, domin kuwa ya san matsayin salla a wurin musulmi.
Kimbal ya ce idan lokacin salla ya yi, musulmi yana bukatar ya samu wani kebantaccen wuri domin ganawa da ubangijinsa, kuma yana bukatar wurin ya zama shiru babu kwaramniya, domin ya samu damar yin tunani kan ibadarsa.
Ya kara da cewa wannan ya kara tabbatar da cewa jami'ar tana bukatar ganin ta fadada alaka tsakaninta da dukkanin bangarori ba tare da wani banbanci ba, ta yadda kowane addini ko al'ada za su iya samun wuria cikin jami'ar.