IQNA

Gambia Ta Zama Jamhuriyar Muslunci

23:22 - December 12, 2015
Lambar Labari: 3462300
Bangaren kasa da kasa, shugaban Gambia Yahya Jammeh ya bayyana kasar a matsayin kasar Musulunci, tare da tabbatar da cewa yana fatan ganin an kawo karshen duk wani abu mai alaka da mulkin mallaka a kasar.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gioz na Reauters cewa, shugaban ya bayyana hakan ne a jiya.

Ya ce, hakan wani mataki ne da ya dace da ra'ayin musulmi masu rinjaye a kasar, kuma ya ce, wannan zai fitar da kasar daga tasirin mulkin mallaka.

Amma ya ce, za a kiyaye hakkokin dukkan 'yan kasar, shugaban Gambia na ya bayyana kasar a matsayin kasar Musulunci, tare da tabbatar da cewa yana fatan ganin an kawo karshen duk wani abu mai alaka da mulkin mallaka a kasar baki daya

Kashi 95 na mutanen kasar musulmi ne daga cikin mutane miliyan 8.1 da ake da su, ya kuma yi mulkin shekaru 21  a kasar.

Shugaba Jammeh dai ya yi kaurin suna wajen yin irin wadannan ikirari cikin shekaru ashirin da daya da ya shafe yana mulkin kasar.

A shekara ta 2013 ya fitar da Gambia daga kungiyar Commonwealth, yana mai cewa, kungiya ce ta masu goyon bayan mulkin mallaka.

A shekara ta dubu biyu da bakawai  ya yi ikirarin cewa, ya gano maganin da zai warkar da cutar kanjamau mai karya garkuwar jiki.

Daga cikin kasashe 187 na duniya kasar tana a matsayin ta 165 ta fuskar tattalin arziki.

3462232

Abubuwan Da Ya Shafa: gambia
captcha