IQNA

Wasu Maniyyata Daga Gambia Ba Su Samu Tafiya Hajji Ba

20:55 - September 23, 2015
Lambar Labari: 3366901
Bangaren kasa da kasa, kimanin maniyyata 200 daga kasar Gambia da suka shirya domin safke farali a shekarar bana ba su samu tafiya ba.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na iol.co.za cewa, sakamakon wasu dalilai da gwamnatin Saudiyya ta bayar na gyara da kuma wasu dalilan na daba, wasu maniyyata ba su samu tafiya aikin haji ba.

Mahukuntan na Sadiyya sun rage yawan izinin shiga kasar ad suke bayarwa ga maniyyata a kasashen duniya daban-daban, wnda hakan ya sanya a shekarar bana adadin ya ragu matuka.

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa ya bayar da rahoton cewa, wasu daga cikin maniyyata daga kasar Gambia da suka shiya suna jiran tafiya zuwa safke faralia a shekarar bana sun fitar da kuna, saboda rashin samun iznin shiga daga mahukuntan Saudiyyah.

A kowace shekara dai akn samu maniyyata kimanin 5000 daga kasar ta Gambia da suke tafiya domin gudanar da ayyukan hajji da kuma ziyarar wurare masu tsarki acikin Makka da Madina a kowace shekara.

3366796

Abubuwan Da Ya Shafa: gambia
captcha