IQNA

An raba Kwafin Kur'anai Masu tsarki Guda Dubu 40 A Kasar Gambia

23:05 - March 02, 2015
Lambar Labari: 2918921
Bangaren kasa da kasa, an rarraba kwafin kur'ani mai tsarki har guda dubu 40 tare da hadin gwaiwa da cibia Al-salamah ga al'ummar kasar Gambia.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Aloke cewa, babbar cibiyar da ke gudanar da ayyukan alkhairi ta Al-salamah a kasar Gambia ta dauki nauyin raba kwafin kur'ani mai tsarki ga al'ummar  kasar kyuata.

Bayanin ya ci gaba da cewa babbar manufar gudanar da irin wadannan ayuka ita ce yada koyarwar addinin muslunci a tsakanin al'ummar kasar wadda ked a matukar kishin addinin muslunci da nem,an sanin hakinin koyarwarsa, inda baya ga hakan ba takan gina masallatai.

Baya ga haka kuma wannan cibiya tana gudanar da wasu ayyukan na musamman da suka hada da daukar nauyin dalibai masu kwazo zuwa kasashen ketare domin kara karatu, tare da bayar da kyautuka ga wadanda suka yi kokari.

Kasar Gambia dai tana yammacin nahiyar Afirka ne, kuma bababn birnin kasar shi ne Banjul, kimanin kashi 90% na daukcin al'ummar kasar dai mabiya addinin muslunci ne.

2917683

Abubuwan Da Ya Shafa: gambia
captcha