IQNA

Vatican Da Kuma Jami’ar Azhar Sun Tattauna Kan Fataucin ‘Yan Dam

21:42 - December 03, 2014
Lambar Labari: 2614986
Bangaren kasa da kasa, babbar fadar mabiya addinin kirista ta Vatican tare da babbar cibiyar addinin muslunci ta Azhar sun cimma matsaya domin yaki da fataucin dan adam.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Youm Sabi cewa fadar mabiya addinin kirista ta Vatican tare da babbar cibiyar addinin muslunci ta Azhar sun cimma matsaya domin yaki da fataucin dan adam wanda yake faruwa a halin yanzu a duniya.
Malamai da shugabannin addinai daban-daban na duniya sun yi Allah da abin da suka kira sabon nau’in bauta na zamani suna masu kiran da a dau matakai na gaba daya wajen kawo karshen wannan lamari a duk fadin duniya.

A jiya Talata ce dai malamai da shugabannin mazhabobin Musulunci na Shia da Sunna, haka nan da malaman darikokin Kiristanci na daga Katolika, Angilika bugu da kari kan yahudawa da mabiya addinan Hindu da Buddha suka taru a fadar Vatican ta mabiya darikar Katolika don tattaunawa hanyoyin da za a ‘yantar da sama da mutane miliyan 36 da aka ce suna cikin kangin bautaa duk fadin duniya.

A karshen taron dai wanda ya samu halartar Paparoma Francis, shugaban mabiya darikar Katolika ta duniya da kuma Ayatullah Muhammad Taqi Modarresi daya daga cikin manyan maraja’an duniyar Shi’a, mahalarta taron sun fitar da sanarwar bayan taro inda suka sha alwashin yin dukkanin abin da za su iya wajen kawo karshen bauta kafin shekara ta 2020.

A watan Nuwamban da ya gabata ne Cibiyar mai fada da bauta a duniya ta fitar da wani rahoto inda tace akwai kimanin mutane miliyan 36 da suke cikin kangin sabuwar bauta. Ita dai wannan kalma ta sabuwar doka ta hada da tilasta wa mutum yin aikin da ba a san ransa ba, ko kuma auren dole, tilasta wa kananan yara shiga cikin yaki, sanya mata cikin ayyuka na lalata don neman kudi da su da dai sauransu inda kasar Indiya take kan gaba a wannan fagen.

2614211

Abubuwan Da Ya Shafa: vatican
captcha