IQNA

An Fara Gudanar Da Gasar Karatu Da Hardar Kur'ani A Kasar Gambia

12:47 - March 02, 2014
Lambar Labari: 1381836
Bangaren kasa da kasa, kamar yadda aka saba a kowace shekara ana gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki a kasar Gambia abangarorin karatu da kuma harda a wannan shekara ma shirin ya ci gaba da gudana kamar yadda aka saba.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na All Africa cewa, an fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki a kasar Gambia  abangarorin karatu da kuma harda tare da halartar malamai da kuma daliban makarantu.

Rahoton ya ce tun kimanin shekaru 15 da suka gabata ne aka fara aiwatar da shirin karkashin kulawar shugaban kasar, wanda ya samu karbuwa a wajen al'ummar kasar matuka, inda adadin mahalarta taron gasar karatun kur'anin ke ninnikawa a kowace shekara.

Bayanin ya kara da acewaa  shekarar bana dubban mutanen suke halartar wannan taro na gasar daga sassa daban-daban na kasar, yayin da malamai da suke wurin suka gabatar da jawabai da suka shafi addinin musulunci, da kuma fadakar da al'umma kan hukunce-hukunce da kuma batutuwa na kyawawan dabi'u na musulunci.

Gambia na daga cikin kasashen musulmi a nahiyar Afirka da ke bayar da muhimmanci matuka ga harkar karatun kur'ani mai tsarki tare da kokarin yada koyarwarsa a tsakanin a'ummar kasar.

1381287

Abubuwan Da Ya Shafa: gambia
captcha