IQNA

Iran Ta Mayar Da Martani Kan Rahoton EU Dangane Da Hakkokin Mata A Kasar

22:08 - September 23, 2019
Lambar Labari: 3484078
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya mayar da martani dangane da rahoton majalisar kungiyar tarayyar turai da ya zargi kasar Iran da take hakkokin mata.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a birnin Tehran, Sayyid Abbas Musawi Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa, kasarsa tana kare hakkokin mata fiye da kowace kasa a yankin gabas ta tsakiya.

Ya ce rahoton na majalisar kungiyar tarayyar turai ko dai ya ginu ne a kan jahilci da rashin sanin hakikanin abin da yake faruwa a kasar dangane da kare hakkokin mata, ko kuma hakan magana ce da take da alaka da siyasa.

Musawi ya ce Iran tana bin tsari ne wanda ya ginu a kan koyarwa ta musulunci, saboda haka duk wani ya ginu a kan wannan mahanga, ba bisa abin da kasashen turai suke kallonsa a matsayin hakkin mata ba, na mayar da su  tamkar kayan talla a kamfanonin da nuna tsiraici.

Kasar Iran dai tana wajabta saka tufafi mai rufe jiki ga mata a kasar, a lokaci guda kuma matan suna da hakkin su yi aiki a dukkanin wurare amma da sharadi saka sutura mai rufe jiki da kuma yin lullubi, wanda hakan yasa matan suka samu damar shiga a dama da su a  dukkanin bangarori na ayyuka da kuma bincike na ilimi, ta yadda hatta bangaren ayyukan jiragen sama, akwai mata matuka jirgin sama a kasar a halin yanzu.

3844273

 

captcha