IQNA

Gargadin Dakarun Yemen Ga Masu Kai Musu Hare-Hare

20:28 - September 19, 2019
Lambar Labari: 3484066
Kakakin dakarun kasar Yemen ya gargadi Saudiyya da UAE da cewa idan suna son su zauna lafiya su daina kai hari a Yemen.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kakakin Sojin kasar Yemen ya fitar da sabbin bayanai kan harin da jiragen yakin kasar marasa matuka suka kai kan cibiyoyin sarrafa man fetir na kasar Saudiya

Kamfanin dillancin labaran Irna ya habarta cewa a jiya Laraba kakakin rundunar tsaron kasar Yemen Yahaya Sari'i ya kira taron manema labarai inda ya bayyana musu hujjojin dake tabbatar da cewa su ne suka kai hari kan cibiyoyin sarrafa man fetir din saudiya.

Yahaya Sari'i ya ce sabin jiragen kasar marasa matuki na da karfi daukan rokoki guda hudu wanda kuma kowannansu ke dauke da bam din Cluster.

Har ila yau Sari'i ya bayyana yadda jiragen suka dauko hoton wuraren da za a kaiwa hari na ciboyoyin man fetir din kasar Saudiyar kafin kai harin.

Wannan na a matsayin mayar da martani kan sanarwar da ministan makamashin kasar Saudiya ya yi na cewa nan da 'yan kwanaki, cibiyoyin man kasar za su koma suna aikinsu, kamar yadda suke baya, don haka, barnar da harin ya janyo ba ta da yawa sosai, tare da zarkin kasar Iran da hanu a kai harin.

A bangare guda kuma Dakarun kasar ta Yemen sun gargadi Hadadiyar daular larabawa da ta fice daga cikin kasar, idan kuma ba haka ba, to nan gaba kadan za ta fuskanci irin harin da aka kai cibiyoyin sarrafa man kasar Saudiya.

3843232

 

 

 

captcha