IQNA

Dakarun Yemen: Za Mu Ci Gaba Da Mayar Da artani A Kan Duk Wani Harin Saudiyya

23:01 - September 17, 2019
Lambar Labari: 3484059
Bangaren kasa da kasa, a daren Asabar da ta gabata ce sojoji da dakarun sa kai na Yemen suka kaddamar da harin ramuwar gayya a kan Saudiyya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, wadannan hare-hare dai an kaddamar da su ne da jirage marassa matuki a kan wuraren sarrafa albarkatun danyen man fetur na babban kamfanin mai na kasar Saudiyya da suke a yankunan Abqaiq da kuma Khurais a gabshin kasar ta Saudiyya.

Hare-haren sun yi sanadiyyar tashin gobara a wuraren, inda tataccen man fetur kimanin lita miliyan biyar ya kama da wuta kuma ya kone, an kuma dauki lokaci kafin a iya shawo kan gobarar.

Mai magana da yawun dakarun kasar Yemen Brigadier General Yahya Sari ya bayyana cewa, an kwashe tsawon kusan shekaru biyar a jere Saudiyya tana kaddamar da hare-hare ta sama da kasa da kuma ta ruwa a kan al’ummar kasar Yemen, tare da kashe dubban fararen hula da suka hada da mata da kananan yara, tare da rusa daruruwan masallatai, makarantu, kasuwanni, cibiyoyin kiwon lafiya, tashoshin wutar lantarki da na makamshi, da madatsan ruwa, tare da rusa dubban gidajen jama’a, ya ce babu wani abu mai amfani a kasar Yemen wanda ya rage a halin yanzu wanda Saudiyya ba ta rusa shi ba, kuma tana ci gaba da yin hakan a kan idanun duniya ba tare da wata kasa tace uffan ba.

Ya ce mayar da martani shi ne kawai zabin da ya rage ga al’ummar Yemen, kuma matukar dai Saudiyya ba ta dakatar da kaiwa al’ummar kasar Yemen hari ba, to kuwa lokaci ya wuce da za ta kawo hari kan kasar Yemen ba tare da ita ma ta fuskanci martani ba.

Wasu daga cikin jami’an gwamnatin Amurka sun zargi jamhuriyar musulunci  da hannu acikin harin, kamar yadda shi ma a nasa bangaren shugaban kasar ta Amurka ya tuntubi yariman Saudiyya mai jiran gado ta wayar tarho.

A nata bangaren jamhuriyar muslunci a ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa, zargin da Amurka ta yi wa kasar Iran babu wani dalili a kansa, kuma hakan yana da alaka ne da siyasar Amurka ta ci gaba da tatsar arzikin kasashen yankin.

Ya ce kasar Yemen tana fuskantar hare-hare tsawon shekaru biyar daga Saudiyya, saboda haka ba abin mamaki ba ne idan Saudiya ta fuskanci hare-haren ramuwar gayya daga al’ummar kasar Yemen kan abin da take aikatawa a kansu, kuma abin mamaki yadda ake ta maganar an kai hari kan kamfanin mai na Saudiyya, amma ba a magana kan hare-haren Saudiyya da kisan dubban mutane da ta yi a Yemen kuma take ci gaba da yi a kullum rana tsawon kusan shekaru biyar a jere.

 

3842547

 

 

 

 

captcha