IQNA

Jagora: Jami’an Iran Sun Yi Ittifakin Cewa Babu Tattaunawa Da Amurka

22:51 - September 17, 2019
Lambar Labari: 3484058
Bangaren siyasa,  jagora Ayatollah Sayyid ali Khamenei ya bayyana cewa dukkanin jami’an gwamnatin kasar sun gamsu da cewa babu wata tattaunawa da Amurka.

Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta cewa, Jagoran juyin juya halin musulinci Ayatollah Sayyid ali Khamenei ya bayyana cewa; siyasar karin matsin lamba kan al’ummar Iran, ba shi da wani tasiri, kuma dukkanin jami’an gwamnatin kasar sun gamsu da cewa babu wata tattaunawa da Amurka, matukar dai ba ta koma cikin yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa tsakanin Iran da manyan kasashen duniya ba.

A yayin da yake gabatar da jawabi na farkon fara karatun sabuwar shekara, jagoran juyin juya halin musulinci Ayatollah Sayyid Ali Khamenei yayi ishara kan basirar al’ummar Iran a game da makarkashiyar makiya cikin shekaru 40 da suka gabata, inda ya ce dogaro da matasa da kuma karkafafa masana’antun cikin gida shi ne hanyar magance matsalolin dakasar ke fuskanta.

Ya ce ikrarin da kasar Amurka ke yi na komawa kan teburin tattaunawa da kasar Iran, manufar hakan ita ce tilastawa kasar ta Iran bin manufofin Amurka, da kuma tabbatar da cewa matsin lambar tattalin arzikin da take yiwa kasar ya yi tasiri.

A kan haka ya ce; a yau dukkanin jami’an kasar Iran da murya guda suna cewa mahukuntan Amurka ba mutane ba ne masu cika alkawari, kuma ba su gamsu da batun komawa kan teburin tattaunawa da su ba, matukar dai Amurka ba koma cikin yarjejeniyar nukiliya ba.

3842725

 

 

 

 

 

captcha