Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, an gudanar da zaman taron juyayi na ranar Tasu’a a Husainiyar Iamm khomeni da ke birnin Tehran, tare da halartar jagoran juyin juya halin muslucni a Iran, da kuma sauran jami’a gami da al’ummar gari.
A yayin wannan taro dai malamai sun gabatar da jawabai kan matsayin wannan rana da kuma abubuwan da suka faru a ranar Tasu’a wadda ita ce ranar da aka tsananta killace iyalan gidan manzon Allah a karbala, da nufin yi musu kisan gilla kamar yadda ya tabbata a tarihi.
Aghaye Ali wani malami da ya gabtar da jawabi a wurin, ya yi ishara zuwa ga irin darussan da suke a cikin wannan waki’a mai girma a cikin addinin muslunci.
Kamar yadda wasu malam da suka gabatar da nasu jawaban, suka tabo muhimamn abubuwan da suka farua wanann rana bisa dogaro da sahihan ruwayoyi na tarihi.