IQNA

Hana Shawagin Jirage Marassa Matuki A Karbala

23:51 - September 08, 2019
Lambar Labari: 3484028
Bangaren kasa da kasa, an hana shawagin jirage marassa matuki a Karbala a ranar ashura.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, babban sakataren majalisar Karbala Hussain Alabbudi ya bayyana cewa,  an hana shawagin jirage marassa matuki a Karbala a ranar ashura saboda dalilai na tsaro.

Ya ce an dauki wannan matakin ne saboda dalilai na tsaro ga tarukan ashura wanda miliyoyin musulmi suke taruwa a birnin mai alfarma.

Ya kara da cewa, an dauki kwaran matakan tsaro a ciki da wajen birnin domin bayar da kariya ga masu tarukan ziyara a ranar Ashura a birnin na Karbala a wannan rana.

Dangane da matakin hana shawagin jirage marassa matuki kuwa, ya ce wannan hada da jiragen yaki da ma wadanda ban a yaki ba, kuma babu wani jirgi mai matuki ko maras matuki da za a bari ya nufi inda haramin Imam Hussain (AS) da na Abbas (AS) suke.

Ya kammala da cewa a halin yanzu an kammala dukkanin abubuwan da suka kamata na matakan tsaroa  dukkanin fadin birnin.

 

 

3840839

 

 

captcha