IQNA

An Girmama Wadanda Suka Gudanar Da Gasar Kur’ani A Burundi

23:57 - August 29, 2019
Lambar Labari: 3483997
Bangaren kasa da kasa, an girmama wadanda suka gudanar da gasar kur’ani mai tsarki a kasar Burundi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na ioqas.org.sa cewa,a  jiya an gudanar da bukin girmama wadanda suka gudanar da gasar kur’ani mai tsarki a kasar Burundi a karkashin kwamitin malaman musulmi na duniya.

Wadanda suka gudanar da wannan gasa adadinsu ya kai 50 da suka hada da yara maza da kuma ‘yan mata.

An gudanar da gasar a bangarori daban-daban na gasar, da suka hada da harda da kuma karatu,  a bangaren harda an gudanar da hardar dukkanin kur’ani, da kuma juzui 15, da kuma 10 da kuma 5.

Taron kammala wannan gasa ya samu halartar malamai da limamai daga sasas na kasar Burundi, wanda aka gudanara  birnin Bujumbura fadar mulkin kasar, an kuma bayar ad kyautukan ne a nan take.

 

3838453

 

captcha