IQNA

Hojjatol Islam Ra’isi: Sakin Jirgin Ruwan Dole A Biya Tara / Adalci Ne sakon Ghadir

23:55 - August 20, 2019
Lambar Labari: 3483969
Bangaren siyasa, Babban  alkalin Alkalan Kasar Iran ya bukaci a biya diyya game da rike jirgin dakon manfetur na aka yi wanda aka saki daga baya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Alkalin Alkalan Kasar Iran hujatul islam Ibrahim Ra’isi ya bukaci a biya diyya game da rike jirgin dakon manfetur dinta da da aka yi wanda aka saki daga baya baya inda yace dole kasar Birtaniya ta biya wannan diya.

Dakarun sojojin ruwa na kasar Birtaniya ne suka rike jirgin dakon manferut din kasar Iran dake dauke da ganganar danyen manfetur miyilan biyu da rabi, tun 4 ga watan yuli da ya gabata, da zargin cewa zai kai man ne zuwa kasar Siriya da hakan ya karya takunkumin da kungiyar tarayyar turai ta kakakabawa kasar Siriya,

Tuni da kasar Iran ta musanta wannan dalilin tare da bayyanashi a matsayin zargi ne kawai mara tushe , kuma Iran ba mamba bace a kungiyar tarayyaar turai EU don haka wannan takunkumin ba zai hau kanta ba, baya ga haka ma tun asali jirgin ruwan ba kasar Siriya zai je ba. Tuni dai aka canzawa jirgin dakon mai din suna bayan da aka sakeshi,

Har ila yau Ra’isi ya bayyana cewa sakin jirgin kwai bai wadatarba, dole ne wadanda ke da hannu wajen abin da ya bayanashi a matsayin fashin doron ruwa su biya diyya na asarar da suka jawo na tsawon lokacin da suke rike da jirgin, domin ya zama darasi ga duk wata kasa dake taka dokokin kasa da kasa,

Daga karshe kasar Iran ta ja kunne Amurka game da duk wani yunkuri na sake kama jirgin.

 

3836199

 

 

captcha