IQNA

An Maraba Da Kafa Gwamnatin Hadaka A Sudan

23:36 - August 18, 2019
Lambar Labari: 3483961
Bangaren kasa da kasa, Yusuf in Ahmad Alusaimin ya yi maraba da kafa gwamnatin hadaka a Sudan.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Yusuf in Ahmad Alusaimin babban sakataren kungiyar OIC ya yi maraba da kafa gwamnatin hadaka a Sudan.

Sojoji masu mulki da kuma gamayyar jam’iyyun adawa a kasar Sudan sun cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin Hadaka wadda za ta hada dukkanin bangarorin.

A jiya ne aka gudanar da gagarumin biki a birnin Khartum fadar mulkin kasar ta Sudan domin rattaba hannu kan wannan yarjejeniya, bikin da ya samu halartar baki daga kasashen ketare, da suka hada da shugabannin kasashe da kuma shugabannin gwamnatoci.

Sojoji da kuma gamayyar kungiyoyi masu neman canji na dimokradiyya a Sudan, sun rattaba hannu kan kafa gwamnatin Hadaka, inda za a kafa majalisar tafiyar da kasar wadda za ta kunshi sojoji 5 da kuma farar hula 6 har zuwa lokacin da za a gudanar da babban zabe a kasar a fiye da shekaru uku masu zuwa.

Wannan na a matsayin wani mataki da ake ganin zai kawo karshen dambarwar siyasa da kasar ta fada tun bayan da sojoji suka kwace mulkin kasar, bayan hambarar da tsohon shugaban kasar Omar Hassan Albashir, biyo bayan zanga-zangar da al’ummar kasar suka share tsawon watanni suna gudanarwa, sakamakon matsaloli da kuncin rayuwa da suka shiga a lokacin mulkinsa.

 

3835685

 

captcha