IQNA

Gwamnatin Iran Ta Yi Maraba Da Matakin Fitar Da Sheikh Zakzaky

22:30 - August 13, 2019
Lambar Labari: 3483944
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Iran ta yi maraba da matakin fitar da Sheikh Zakzaky tare da mai dakinsa zuwa India.

Kamanin dillancin labaran iqna, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Sayyed Abbas Musawi ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran ta yi maraba da matakin da gwamnatin Najeriya ta dauka na bayar da dama ga sheikh Ibrahim El-zakzaky, shugaban harka Islamiya IMN domin zuwa kasar Indiya, domin neman magani.

Tashar talabijin ta Al-Alam ta nakalto Abbas Musawi yana fadar haka a safiyar yau Talata, ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar Iran a shirye take ta taimaka da duk abin da zata iya domin samun lafiyar malamin.

Musawi ya yi fatar Sheikh Zakzaky zai sami lafiyar a wannan tafiyar, sannan yana saran za a warware matsalar da ke tsakanin Harkar Musulunci da mahukunta a Najeriya, dangane matsalolin da suka yi ta tasowa a tsakaninsu a shekarun da suka gabata.

Har’ila yau Musawi ya yi fatan gwamnatin tarayyar Najeriya zata kare hakkokin mabiya mazhabar shi’a a kasar, sannan ta kuma dauke haramcin da ta dorawa harka Islamiyya ko IMN a baya-bayan nan.

 

3834602

 

captcha