IQNA

Sabon Bangaren Bincike Kan Ilmomin Kur’ani A Saudiyya

23:57 - August 06, 2019
Lambar Labari: 3483920
Bangaren kasa da kasa, ma’aikatar kula da harkokin ilimi a Saudiyya na shirin samar da bangaren bincike kan ilmomin kur’ani a wasu jami’oin kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a wani rahoto da shafin abudhabinews.com ya bayar, an bayyana cewa ma’aikatar kula da harkokin ilimi a Saudiyya na shirin samar da bangaren bincike kan ilmomin kur’ani a wasu jami’oin kasar nan ba da jimawa ba.

Bayanin ya ce wannan shiri zai bayar da damar gudaar da bincike mai zurfi kan ilmomin kur’ani, da kuma samar da hanya ta rage samun sabani a kan wasu mas’aloli na kur’ani musamman kira’oi.

Yanzu haka dai an fara daukar sunayen mutanen da suke son yin rijista domin shiga wanann shiri, wanda zai farad a zaran ma’aikatar ilimin kasar ta kammala shirinta tare da jami’oin da za su dauki nauyin shirin.

Da dama daga cikin jamioin da suke kula da harkokin bincike kan ilmomin addini, suna bayar da muhimamnci ne a bangarori na hadisi da fikihi da sauran bangarori, yayin da a ilimin kur’ani bahasin kira’oi bakasafai ake bashi muhimamnci a wadannan jami’oi ba, wanda kuma shi ne dalilin bullo da wannan shiri.

 

3832776

 

 

 

captcha